Akalla malaman makaranta 2,000 ne aka kashe baya ga wasu 19,000 da aka raba da muhallinsu sakamakon ta’addancin ’yan bindiga daga shekarar 2014 zuwa yanzu a Najeriya.
Shugaban Shirin Zaman Lafiya Da Cigaban Manoma Da Makiyaya ta Afirka (FHIPPDAFRICA), Salim Umar, ya ce ’yan ta’adda sun lalata makarantu sama da 1,500 a shekara takwas din da suka gabata.
- An kashe shugaban ’yan bindiga Dogo Maikasuwa a Kaduna
- Yadda aka sace matafiyan Taraba 19 a Nasarawa
Ya ce, “Uwa uba shi ne matsalar ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane da suka lakume rayuka mutane da dabbobi, gami da hana noma da kiwo.”
Wannan a cewarsa, ya haifar da karuwar yara marasa zuwa makaranta da raguwar wadanda ake sanyawa a makarantun ’ya’yan makiyaya.
Ya bayyana cewa a shekaru 10 zuwa 15 suka gabata, matsalar tsaro a yankin Arewa ta haifar da sabuwar barazana ga ilimin makarantun ’ya’yan makiyaya.
Ya yi wannan batu ne a makalar da ya gabatar kan tasirin ayyukan ’yan bindiga ga aikace-aikacen Hukumar Ilimin ’Ya’yan Makiyaya, a lokacin taron horo da hukumar ta shirya wa ma’aikatanta kan tattara bayanai.
Shugaban Hukumar, Farfesa Bashir Usman, ya ce an shirya horos ne domin nuna wa jami’an hukumar hanyoyin tattara bayanai da alkaluma da za su taimaka wajen gano ainihin sabubban rikice-rikice da matsalolin tsaro.
Ya ce daga abin da taron ya gano ya kuma tattauna a kai, za su bai wa al’ummomi dabarun da za su yi amfani da su wajen dakile rikice-rikice.