A daren Lahadin da ta gabata ce wadansu ’yan bindiga suka hallaka wata mai ciki da mutum 15 a garin Numa da ke Karamar Hukumar Akwanga a Jihar Nasarawa.
Rahotanni sun ce ’yan bindigar sun kai hari ne a lokacin da jama’a suka taru don radin suna inda akalla mutum 14 suka samu raunuka daban-daban.
Shugaban Kungiyar Miyetti Allah ta Jihar, Alhaji Muhammad Hussaini ya tabbatar da faruwar lamarin. ya ce maharan ba Fulani ba ne face ’yan ta’adda “Na yi imani maharan ba Fulani ba ne, ’yan ta’adda ne daga suka fito daga sassan kasar nan,” inji shi.
Sai ya yi kira ga jami’an tsaro su binciko wadanda suka aikata wannan mummunan aiki don a hukunta su.
Sanata mai wakiltar Nasarawa ta Arewa, Philip Gyunka ya ce, “Wannan hari ne na kisan gilla a kan wadanda ba su ji ba, ba su gani ba, inda aka kashe daukacin iyali guda tare da wani tsoho dan shekara 100.”
Sanatan ya ce a baya ya shigar da kudiri a majalisa a kan ya kamata gwamnati ta samar da wani sansani na soji a garin Akwanga domin a cewarsa Akwanga hanya ce ta matafiya daga sassa daban-daban na kasar nan da take sada su da Abuja.
Sanatan ya kara da cewa yawan garkuwa da mutane da fashi da makami a kan hanyar Akwanga zuwa Abuja yana faruwa ne saboda kai-kawon makamai a hanun mutane ba tare da tantancewa ba.
Ya ce samar da sansanin sojin zai taimaka wajen tabbatar da tsaro a yankin. Ya yi kira ga gwamnati da ta dauki mataki a kan garkuwa da mutane da hare-haren da ake kai wa wasu al’ummomi.
Sanatan ya ce a makon jiya ne ya gabatar da kuduri a gaban Majalisar Datawa a kan harin da ake zargin Fulani makiyaya suna kaiwa kauyukan Mante daNindan da kuma Katanza.
Ya yi kira ga Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta taimaka wa wadanda harin ya rutsa da su. Ya ja hankalin hukumomin su dauki tsauraran matakai wajen hana jama’a mallakar makamai ba bisa ka’ida ba.
Shugaban kabilar Mada, Cif Samuel Gamu ya bayyana cewa suna da kiddidigar mutuwar mutum 15 da kuma wadansu da dama da suka samu munanan raunuka. Ya ce kafin faruwar al’amrin maharan suna tare ne da masu bikin radin sunan amma daga baya suka rika yin harbin kan mai uwa da wabi. Ya ce an samu nasarar gano wadansu daga cikin maharan kuma tuni aka mika sunayensu ga jami’an tsaro.
Yayin da aka tuntubi Mataimakin Kwamishinan ’Yan sanda mai kula da kai samame DSP Umar Shehu Nadada ya tabbatar da faruwar al’amarin.
Tuni Gwamnan Jihar Umaru Tanko Al-Makura ya ba jami’an tsaro umarnin su gaggauta zakulo wadanda suka kai harin domin gabatar da su a gaban kotu a yi musu hukunci.