✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahara sun kashe mahaifin shugaban karamar hukuma a Kano

Wasu ’yan bindiga sun harbe mai unguwar Maigari a Karamar Hukumar Rimin Gado ta Jihar Kano, Alhaji Dahiru Abba a gidansa.

Wasu ’yan bindiga sun harbe mai unguwar Maigari a Karamar Hukumar Rimin Gado ta Jihar Kano, Alhaji Dahiru Abba a gidansa.

Dansa, wanda shi ne Shugaban Karamar Hukumar Rimin Gado, Barista Munir Dahiru Maigari, ya shaida wa wa Aminiya cewa sai da maharan suka yi wa mahaifin nasa raunuka da dama sannan suka harbe shi har lahira.

Shugaban karamar hukumar ya ce, “Da misalin karfe 2 na dare ne maharan suka zo har gida suka yi wannann aika-aika.

“Ba za mu iya cewa komai game da abin da a faru ba, amma ya riga ya rasu, kuma muna rokon Allah Ya yi masa rahama.”

Wakilinmu ya tuntubi kakakin ’yan sanda na Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, wanda ya ce ba shi da labari, amma zai bincika.