✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun kashe magidanci bayan karbar N1.7m a Zariya

’Yan bindigar sun harbe magidancin sannan suka bar dansa a raye.

’Yan bindiga sun kashe wani magidanci bayan sun karbi kudi fansa Naira miliyan 1.7 da sabon babur daga hannun iyalansa a yankin Zariya na Jihar Kaduna.

A ranar 2 ga watan Disamba 2021 ’yan bindiga suka afka wa unguwanni hudu ne da ke yankin Dutsen Abba, inda suka kashe tsohon Kansilan Dutsen Abba, Usman Ibirahim.

Daga nan ne suka yi awon gaba da wani magidanci mai suna Alhaji Dahiru da Alhaji Shaibu da matarsa mai suna Hajiya Zainab mai tsohon ciki da kuma dansa.

Bayanan da Aminiya ta samu daga al’ummar yankin na cewa a ranar Litinin 27 ga watan Disamba 2021, bayan ya kwashe kwanaki 25 a hannunsu, ’yan bindigar suka kashe Alhaji Dahiru bayan sun sako shi tare da dansa, kuma suka rako su har kusa da garin Galadimawa, inda a nan ne suka harbe shi, suka kyale dan nasa ya dawo.

Sai dai kuma sun ci gaba da tsare matarsa Hajiya Zainab mai dauke da tsohon ciki a can hannunsu.

Al’ummar yankin sun ce an tura wasu mutane zuwa dauko gawarsa domin a yi masa jana’iza, kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.

Don haka sun roki jama’a da su rika sanya su cikin addu’a domin samun saukin halin da yankin ke ciki na rashin kwanciyar hakali.