A ranar Lahadi ne wasu ’yan bindiga suka kashe mutum 11 ciki har da wata mata mai juna biyu a kauyen Ole’Adag’aklo a Ƙaramar hukumar Agatu ta jihar Benuwai.
Mazauna yankin sun ce ’yan bindigar sun kai harin ne da yamma inda suka yi ta harbin kan mai uwa da wabi, suka kashe mutum 11 tare da yin awon gaba da wasu.
- Jami’an DSS sun yi watsi da alkali, sun yi kame a harabar kotu
- Yadda aka kama ‘dan kunar bakin wake’ dauke da bom a banki a Jos
Shugaban Ƙaramar Hukumar Agatu, Yakubu Ochepo, wanda ya tabbatar wa wakiliyarmu lamarin ta wayar tarho a ranar Litinin ya ce, “an kashe mutane 11.
Daga cikin adadin, an gano gawarwaki bakwai, ciki har da ta wata mata mai juna biyu da dattijo da wasu matasa biyar.
Sojoji sunsamu nasarar ƙwato sauran gawarwaki huɗu.
“Sojoji sun ziyarci wajen a ranar Lahadi domin ƙwato gawarwakin. An yi harbe-harbe kuma ’yan bindigan da ke ɗauke da makamai sun gudu suka sake haɗuwa.
“Ina Makurdi yanzu don bayar da rahoto ga jami’an Operation Whirl Stroke (OPWS). Muna buƙatar ƙarin ka jami’ah gefe. Mun ji sun kuma kama wasu a raye suka jefa wasu cikin kogin.”
Bayan tuntuɓar Kakakin ‘yan sandan jihar, SP Catherine Anene, ta ce ba a sanar da ita lamarin ba.