Wani Jami’in Hukumar Yaki da Wa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa (EFCC), da ke Makurdi a Jihar Benuwai, ya musanta cewar hukumar ta gano buhunan wasu tsofaffin takardun Naira tare da kama wasu wadanda ake zargi da wajen boye kudin.
A yammacin ranar Talata ne wani bidiyo ya karade kafafen sadarwa kan adda aka gano buhunan tsofaffin kudaden Naira da ake zargin jami’an EFCC sun kwato a kasuwar Wadata da ke birnin Makurdi a jihar.
- DAGA LARABA: Yadda Talla Ke Bata Rayuwar Yaran Arewa
- Qatar 2022: Yadda Faransa da Maroko za su barje gumi
Bidiyon ya nuna buhunan tsofaffin takardun kudin cikin wata katon sunduki, wanda ake zargin mallakin wasu mutane ne.
Amma, wani jami’in EFCC wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce faifan bidiyon da ke yawo a shafukan sada zumunta ba gaskiya ba ne.
Ya ce bayan samun labarin kudin ne aka tura jami’an hukumar zuwa wajen, amma abun mamaki sai suka iske cewa kudaden da za a daina amfani da su ne Babban Bankin Najeriya (CBN) ke konewa.
“Gaskiya ne mun samu labarin tsofaffin kudaden kuma mun garzaya kotu don nenan izinin gudanar da bincike, amma muna isa wurin sai muka iske cewar tsofaffin takardun kudin da ake konawa.
“Mamallakin kudin ya ce ya karbo ne daga CBN kuma an musu gutsi-gutsi tun kafin ya kawo su don konawa, don haka ba kudi ne da za a more su ba,” in ji jami’in.
Idan ba a manta ba CBN na ci gaba da kona tsofaffin takardun kudi tun bayan da ta bayar da umarnin sauya fasalin takardun kudin Naira na N200, N500 da kuma N1,000.
Ana sa ran fara amfani da sabbin takardun kudin a ranar Alhamis, 15 ga watan Disamba, a yayin da wa’adin karbar tsofaffin takardun kudin zai kare a ranar 31 ga watan Janairun 2023.