A daren ranar Talata ne wasu ’yan bindiga suka kashe wani lauya da matarsa da wani bako a yankin Agbo dake Makurdi babban birnin jihar Binuwai.
’Yan bindigar sun kashe matar lauyan mai suna Barista Moses Udam, har cikin gida da misalin karfe 11:30 na dare tare da raunata wani mutum daya.
- Bakuwar cuta ta kashe mutum 17 a Benuwe
- An yi garkuwa da likitoci biyu da ma’aikacin asibiti a Benuwe
Aminiya ta gano cewa mamacin ya yi bikin murnar zagayowar ranar haihuwarsa a ranar, kafin daga bisani ’yan bindigar su zama ajalinsa.
Rahotanni sun ce jim kadan da faruwar lamarin rundunar soji ta bayyana a wajen, kafin zuwan jami’an ‘yan sanda wanda daga nan suka kwashe gawarwakin zuwa asibiti.
Da wakilinmu ya tuntubi kakakin ’yan sandan jihar DSP Catherine Anene, ta tabbatar da faruwar lamarin.
Catherine ta ce harin ’yan bindigar ya yi sanadin rasa rayukan mutum biyu, guda kuma na Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar (BSUTH), inda yake ci gaba da murmurewa.