Wasu ’yan bindiga sun harbe jami’ai uku na Hukumar Yaki da Shan Miyagun Kwayoyi ta NDLEA a garin Okene.
Kwamandan rundunar hukumar da ke jihar Kogi, Alhaji Idris Bello ya fada wa manema labarai a jiya a garin Lokoja cewa ’yan bindigar sun harbe jami’an ne yayin da suke bakin aiki a yankin.
Ya bayyana cewa ’yan bindigar wadanda suka dirarwa jami’an ba zato-ba tsammani sun budewa jami’an wuta da misalin karfe takwas da rabi na dare a ranar 13 ga watan Oktoba in da nan take suka mutu.