✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Yan bindiga sun kashe gomman mutane a Zamfara

Gomman mutane sun rasa rayukansu a sanadiyar harin.

‘Yan bindiga sun kashe gomman mutane da dama yayin da suka kai hari kan mazauna kauyen Jaya da ke gundumar Boko a Karamar Hukumar Zurmi ta Jihar Zamfara.

Bayanai sun ce Jaya wani kauye ne da ke da tazarar kilomita kadan da Gabashin Boko, inda ‘yan bindigar suka kashe mutane da dama yayin da wasu suka jikkata.

  1. Rundunar ‘yan sandan Kano ta gayyaci Muhuyi Magaji
  2. ‘Buhari ya mayar da Fadar Shugaban Kasa hedikwatar APC’

Mashaida lamarin sun shaida wa Aminiya cewa ‘yan bindigar sun kai harin ne haye a kan babura fiye da dari.

“Sun kuma kwashe mana shanu da sauran dabbobin kiwo da dama.

“Na ga mutane uku da suka ji rauni a kafa da cinyoyi wadanda tuni an kai su asibiti garin Boko.

“Sai dai saboda yawan mutanen da lamarin ya shafa, an garzaya da was su zuwa wani asibiti mafi girma.

“Kwanakin baya ma ‘yan bindiga sun yi kokarin kai hari amma wasu ‘yan sa-kai suka dakile yunkurin nasu.

“Hakan ne ya fusata ‘yan bindigar shi ne suka sake yin shiri suka dawo.

“Yan bindigar masu yawan gaske haye a kan babura fiye da 100 sun rika shiga har gidajen mutane suna fito da su.

“Mata da yara da dama sun tsere daga garuruwan kuma wasu daga cikinsu sun fake a Boko,” a cewar wani mazaunin garin mai suna Ali Aminu.

Sai dai kokarin da wakilinmu ya yi na jin ta bakin Kakakin ‘Yan sandan Jihar Zamfara, SP Muhammad Shehu ya ci tura.