✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe direba sun sace dalibai uku a Kaduna

Wasu da ake zargin ’yan ta’addan Birnin Gwari ne sun halaka wani direba sannan suka sace wasu dalibai uku a hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna.…

Wasu da ake zargin ’yan ta’addan Birnin Gwari ne sun halaka wani direba sannan suka sace wasu dalibai uku a hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna.

Lamarin ya auku ne a ranar Asabar da misalin karfe uku na rana a lokacin da suke kan hanyarsu ta komawa gida Birnin Gwari bayan sun zo sun rubuta Jarrabawar Shiga Jami’o’i da Manyan Makarantu ta Kasa (JAMB).

Direban da aka kashe mai suna Ibrahim Dowa, yana aiki ne da tsohon Dan Majalisar wakilai ne Hassan Adamu Shekarau.

Kakakin ’yan sandan jihar ASP Mohammed Jalige, ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Ya ce, akalla mutum hudu aka sace a cikin motar bayan sun halaka direban motar.