✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun kashe daliban Jami’ar da suka sace Kaduna

An tsinci gawar wasu daga cikin daliban Jami'ar Greenfield a wani kauye da ke kusa da ita.

’Yan bindiga sun kashe uku daga cikin daliban da suka yi garkuwa da su a Jami’ar Greenfield da ke Jihar Kaduna.

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar, Samuel Aruwan ya sanar cewa an tsinci gawar daliban uku ne a kauyen Kwanar Bature da ke kusa da Jami’ar a ranar Juma’a.

Bayanin na Aruwan na zuwa ne kwana uku bayan garkuwa da daliban, wadanda gwamnatin Jihar ta ce ba ta kai ga tantance hakikakin yawansu ba.

An sace daliban ne kimanin wata biyu bayan ’yan bindiga sun kutsa cikin Kwalejin Koyar da Dabarun Gandun Daji ta Tarayya da ke Jihar, suka yi awon gaba da dalibai 39, kafin daga baya su sako 10 daga cikinsu, baya iyayensu sun biya kudaden fansa.

Gwamnanin Jihar Kaduna ta yi watsi da tattaunawa da masu garkuwar ko biyan su kudin fansa, tsare da shan alwashin hukunta duk wanda ta samu da yin hakan da sunanta.