✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun kashe Dagaci da wasu mutum 5 a Katsina

'Yan bindigar sun kashe dagacin Daddara tare da wasu mutane.

Rahotanni daga Jihar Katsina sun ce da sanyin safiyar Alhamis, wasu ’yan bindiga suka farmaki kauyen Daddara da ke Karamar Hukumar Jibiya, inda suka kashe mutum shida, cikinsu har da Dagacin garin.

Maharan sun kuma sace karin wasu mutum biyar, kamar yadda wani daga cikin mazauna kauyen na Daddara ya tabbatar wa Aminiya.

Mutumin, wanda ’yarsa na cikin wadanda maharan suka yi garkuwa da su ya ce, ’yan bindigar sun kashe Dagacin garin, Alhaji Jafaru Rabiu, wanda aka fi sani da Magaji Yangayya da kuma yaron gidansa, Malam Nasir Danye.

“A Daddarar Malamai, sun kashe Dagaci da hadiminsa da kuma wasu mutane sannan sun sace ’yata da ke aure a garin. A nan babban garin Daddara kuma sun kashe mutum hudu sannan suka sace wasu,” inji shi.

Ya kuma ce bayan sace mutanen, wasu da dama sun ji rauni a yunkurin tsira da rayuwarsu.

Har wa yau, ya ce ’yan bindigar sun shiga gida-gida inda suka saci dabobbi, kayan abinci da kuma kudade daga hannun mutanen da suka shiga gidajensu.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton babu wata sanarwa daga rundunar ’yan sandan Jihar ta Katsina, saboda kakakinta, SP Gambo Isah bai daga waya ko amsa rubutaccen sakon kar-ta-kwanan da wakilinmu ya aike masa ba.