✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan bindiga sun kashe basarake a Kebbi

‘Yan bindiga sun kashe Hakimin Bajida, Musa Muhammad Bahago a Karamar Hukumar Fakai ta jihar Kebbi. ‘Yan sanda sun ce ‘yan fashin sun yi ta…

‘Yan bindiga sun kashe Hakimin Bajida, Musa Muhammad Bahago a Karamar Hukumar Fakai ta jihar Kebbi.

‘Yan sanda sun ce ‘yan fashin sun yi ta sarar mamacin da adduna ne har ya mutu a ranar Talata a hanyarsa da komawa gida daga garin Zuru.

Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kebbi, DSP Nafi’u Abubakar ya ce, “‘Yan sanda na da labarin abin da ya faru kuma muna kokarin ganin an hukunta wadanda suka aikata laifin”.

Sai dai ya ce babu wanda aka kama da zargin hannu a aika-aikan sai dai sun dukufa domin ganin an kama masu laifin.

Dan uwan mamacin mai suna Umar Muhammad ya ce lamarin ya faru ne dab da magariba