Wasu ’yan bindiga sun kai hari ofishin ’yan sanda dake Ekori a Karamar Hukumar Yakurr a jihar Kuros Riba tare da kwashe bindigu.
Mataimakin Kakakin ’Yan Sanda na jihar, Igri Ewa ne ya tabbatar da hakan ranar Litinin.
Ya shaidawa ’yan jarida a Kalaba babban birnin jihar cewa ’yan bindiga wadanda ake zargin matsafa ne suka kai hari ofishin ’yan sandan.
Ya kuma ce tuni jami’ansu suka kaddamar da bincike a kan lamarin, yana mai cewa nan ba da jimawa ba rundunar za ta fitar da sanarwa a kan haka.
Sakamakon harin dai, maharan sun yi awon gaba da bindigu kirar AK-47 daga hannun ’yan sandan dake kan aiki a lokacin.
Wani ganau ya shaidawa ’yan jarida cewa maharan sun firgita jami’an ’yan sandan dake aiki ne, suka lakadawa daya daga cikinsu dukan tsiya sannan suka yi awon gaba da wata bindiga kirar AK-47.
Rahotanni sun ce harin ya yi sanadiyyar rufe ofishin ’yan sandan na Ekori har sai abin da hali ya yi, sannan aka umarci jami’an da suke aiki a ciki su koma ofishin Ugep wanda ke shalwakatar Karamar Hukumar.