Wasu ‘yan bindiga sun kashe mutane hudu a wani harin da suka kai kauyukan Daja da Mangun dake Karamar Hukumar Mashegu a jihar Neja.
Wata majiya ta ce ‘yan bindigar sun shiga kauyukan akan babura rike da bindigogi kirar AK 47, inda suka mamaye kasuwar garin Daja da ke karamar hukumar Mashegu ta jihar Neja a yammacin ranar Litinin.
- Gobarar tankar mai ta hallaka mutum biyar a Neja
- ’Yan bindiga: Yadda bayan sulhu a Katsina da Zamfara mahara suka karkata jihohin Sakkwato da Neja
Rahotanni sun ce maharan sun shiga kauyen ne neman wani dan kasuwa mai suna Baira, wanda suka yi rashin sa’a ba su same shi ba.
Hakan ne ya sa suka fusata inda suka hau harbi kan mai uwa da wabi.
A cewar majiyar, ‘yan bindigar sun kashe mutane biyu wanda daga bisani suka tsere zuwa kauyen Mangun.
A wani labarin kuma, wani mazaunin garin Daja da ‘yan bindigar suka afka wa, ya hado ‘yan banga domin tunkarar ‘yan bindigar, amma sun yi rashin sa’a, inda suka rasa mutum biyu, su kuma ‘yan bindigar suka rasa mutum daya.
Shugaban Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja, Alhaji Ibrahim Tanko Inga ya tabbatar da faruwa harin, inda ya ce an shaida wa hukumar ta su faruwar sa.
Sai dai kakakin Rundunar ‘Yan Sandan jihar Neja, ASP Waisu Abiodun bai daga wayar da aka kira sa ba domin jin ta bakinsa kan harin.