Wasu ’yan bindiga sun kai hari Fadar Sarkin Kagara da ke Jihar Neja, Alhaji Ahmadu Attahiru II, da yammacin ranar Talata.
Har yanzu dai babu cikakkun bayanai a kan harin, amma wata majiya ta tabbatar wa da wakilinmu cewa an kai harin ne dab da Sallar Magriba.
- Jirgin yakin sojoji ya hallaka masunta 20 a Borno ‘bisa kuskure’
- A cika alkawarin da aka yi game da Ajaokuta
Sai dai rahotanni sun ce Sarkin ya bar garin zuwa birnin Minna ranar Litinin.
A ranar Juma’ar da ta gabata ne dai aka katse hanyoyin sadarwar garin.
Kazalika, wani dan asalin garin mazaunin Minna ya tabbatar da kai harin.
Ya ce, “Ba zan iya ba ka cikakken bayani ba, saboda mutanen da suka kirani da yamma yanzu lambobinsu ba sa shiga sakamakon katse sabis din garin ranar Juma’a.
“Na tabbatar hatta wadanda suka kira wayar cikin daji suka shiga kafin su sami yin wayar, amma gaskiya ne an kai hari Fadar Sarkin Kagara,” inji shi.
Da wakilinmu ya tuntubi kakakin ’yan sandan Jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, ya yi alkawarin bayar da cikakken bayani daga bisani.