✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun kai hari a Kano

An kai harin bayan Ganduje ya koka cewa ’yan bindiga na taruwa a Dajin Falgore.

’Yan bindiga sun kai hari a Jihar Kano inda suka yi awon gaba da wani attajirin dan kasuwa a Karamar Hukumar Dambatta.

Da tsakar daren ranar Alhamis ne maharan suka kai farmaki a garin Kore da ke Karamar Hukumar, suna luguden wuta babu kakkautawa.

Harin na Dambatta na zuwa ne jim kadan bayan korafin Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje, cewa ’yan bindiga sun fara taruwa a Dajin Falgore da ke Jihar, ya kuma bukaci hukumomin tsaro su gaggauta tarwatsa miyagun tun kafin su yi karfi.

Mazauna garin Kore sun ce hantarsu ta kada matuka da ganin maharan sun kutsa cikin garin a kan babura, suna luguden wuta, lamarin da ya sa wasunsu tserewa zuwa cikin daji a cikin daren.

Sun bayyana cewa babu jami’an tsaro da lokacin da aka kai farmakin tare da yi awon gaba da dan kasuwar.

Sai dai sun ce ba a samu asarar rai ba a harin, in banda wani karamin yaro da ya samu raunin harbin bidiga a kunne.

Shugaban Karamar Hukumar Dambatta, Muhammad Abdullahi Kore, ya tabbatar da sace dan kasuwar a harin da tsakar dare.