✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun harbe matafiya 7 a hanyar Taraba

Mahara sun harbe matafiya bakwai har lahira a safiyar Litinin a kan babbar hanyar Takum zuwa Wukari da ke Jihar Taraba.

Mahara sun harbe wasu matafiya guda bakwai har lahira a safiyar Litinin a kan babbar hanyar Takum zuwa Wukari da ke Jihar Taraba.

Kisan gilla da aka yi wa matafiyan da direban motarsu ya haifar da zaman dar-dar a yankin Takum.

Shaidu sun bayyana wa wakilinmu cewa ɗauƙacin matafiyan waɗanda ’yan garin ne, suna hanyarsu ta zuwa garin Sa’ayi da ke Jihar Binuwai ne lokacin da harin ya rutsa da su a tsakanin garin Chanchangin da garin Wukari.

Wani shaida ya ce maharan sun buɗe wa motar wuta ne suka kashe duk mutanen da ke cikinta, nan take, amma ba su ɗauki komai ba a cikinta.

Ya yi zargin maharan na daga cikin ’yan ta’addan da suka addabi dazukan da ke tsakanin Jihar Binuwai da Jihar Taraba.

A bisa wannan hanya ce dai aka kashe basaraken garin Chanchangi da babban ɗansa a watan Yuli.

Aminiya ta gano cewa hanyar ta zamo tarkon mutuwa saboda ayyukan ’yan ta’adda da ke yin fashi da kuma garkuwa da matafiya domin karɓar kuɗin fansa a cikin dare da yini.

Wakilinmu ya tuntuɓi kakakin ’yan sandan jihar Taraba, DSP kwach,  game da harin na safiyar Litinin, amma jami’in ya ce masa sa zai bincika.