Jami’an tsaro a kasar Mexico sun sanar da mutuwar ’yan sanda 13 na kasar, a wani harin kwanton-bauna da ’yan bindiga suka kai yankin Coatepec Harinas da ke kasar.
Rahotanni sun bayyana cewa daga cikin wadanda suka mutu akwai jami’an ’yan sanda da kuma jami’an ofishin mai gabatar da kara na kasar.
- Yadda dubun mai yi wa yara maza fyade ta cika
- Malaysia ta ba jakadun Koriya ta Arewa sa’o’i 48 su fice daga kasarta
- An cafke dillalin makaman ’yan bindiga a Zamfara
- Yau ce Ranar Barci ta Duniya
Jihar Mexico na daya daga cikin yankunan da ke da hadarin rayuwa saboda hare-haren ’yan bindiga.
Alkaluma sun nuna cewa ya zuwa yanzu an kashe mutane sama da 300,000 tun bayan girke sojoji da gwamnatin kasar ta yi a jihar.
Tun bayan shekara ta 2006 harkar tsaro ta tabarbare a kasar Mexico, inda ’yan bindiga ke cin karensu babu babbaka.
Hakan ya yi sanadin kaurar mutanen kasar da ma wanda ba ‘yan kasar ba zuwa kasashen dake makobtaka da ita.