✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun hallaka Dagaci a Kaduna

Maharan dai sun shiga har cikin gidan mai garin sannan suka bindige shi.

’Yan bindiga sun kashe Dagacin kauyen Dogon Daji da ke Karamar Hukumar Sanga a Jihar Kaduna, Anja Malam.

Rahotanni sun ce ’yan bindiga sun shiga har cikin gidan mai garin sannan suka bindige shi.

Da take tabbatar da kisan, Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce jami’an tsaro sun shaida mata cewa maharan sun hallaka Dagacin na Dogon Daji.

Cikin wata sanarwa da Kwamishinan Tsaro da Al’amuran Cikin Gida na Jihar, Samuel Aruwan ya fitar, Gwamnatin ta ce ’yan bindigar sun kutsa cikin gidan mai garin inda suka harbe shi har lahira nan take.

Sanarwar ta ce, “Gwamna Nasir El-Rufai ya nuna damuwarsa kan harin, sannan ya yi addu’ar Allah Ya jikan Dagacin.

“Ya kuma mika ta’aziyyarsa ga iyalai da al’ummar kauyen Dogon Dajin kan kisan gillar da aka yi wa Dagacin,” inji Kwamishinan.

A karshe ya ce ana gudanar da bincike domin gano wadanda suka aikata kisan gillar.