Kansilan da ke wakiltar mazaba ta 6 a yankin Sagbama da ke Jihar Bayelsa, Karma Agagowei, ya gamu da ajalinsa bayan da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka bude masa wuta.
Agogowei kansilan Jam’iyyar PDP ya gamu da ajalinsa ne a yankin Opolo, a kan hanyarsa ta dawowa daga taron jam’iyyar a daren Asabar.
An garzaya da shi asibiti har sau biyu, asibitin Gloryland da Cibiyar Lafiya ta Gwamnatin Tarayya da ke Yenagoa domin ceton ransa amma bai samu kulawa ba, saboda rashin takardar rahoto na ‘yan sanda, inda ya cika.
Rahotanni sun nuna cewa ‘yan bindigar sun raunata karin wani mutum da ke tare da kansilan wanda ya tsira da mummunan raunin da aka yi masa na sara da adda.