Maharan da suka yi garkuwa da fasinjoji a harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna sun fitar da hotunann fasinojin jirgin da ke hannunsu.
’Yan bindigar sun fitar da hotunan da ke nuna akalla mutum 41 ne ranar Talata, wata guda da sace matafiyan da karfin bindiga a harin bom da suka kai wa jirgin da dare, tare da yi wa fasinjojin ruwan wuta.
- ’Yan ta’adda na shirin kai harin bom a wuraren ibada —DSS
- DAGA LABARA: Yadda Za A Magance Matsalar Tsaro A Arewacin Najeriya —Masana
Hotunan guda biyu da suka bayyana sun nuna maza 17 da kuma mata 19 sai da kananan yara biyar da aka dauke su daban-daban.
Tuni dai aka tabbatar da mutuwar mutum takwas daga cikin fasinjojin jirgin da ’yan bindiga suka kai wa hari ranar 28 ga watan Maris, 2022.
Daga baya ’yan bindigar sun fitar da bidiyon mutanen da ke hannunsu, sannan suki mutum daya, Alwan Hassan, wanda suke ce tsufarsa ce ta sa suka ske shi.
Bayan sako Alwan, wanda shi ne Manajan Daraktan Bankin Noma, rahotanni suka nuna sai da aka biya kudin fansa Naira miliyan 100 aka sako shi.