‘Yan bindiga da suka tuba a jihar Zamfara sun kwato mutum 12 daga hannun masu garkuwa da mutane a jihar.
Tubabbun ‘yan bindiga sun kubutar da mutanen ne a wani harin kwanton bayba da suka kai wa maboyar masu garkuwan.
Hakan na cikin alkawarin da suka yi na taimakawa a yaki abokan tsohuwar mummunar sana’ar tasu da suka bijire wa zaman lafiya.
Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Zamfara Usman Nagoggo ya yaba kokarin musamman yadda suka cika alkawarin da suka yi a sulhunsu da gwamnati.
- An kashe mutum 70 a Sabon Birni bayan ziyarar Gwamna Tambuwal
- Dubun mukarraban kasurgumin dan ta’adda ya cika
- PDP ta yabi yadda Buhari ya tunkari ‘yan bindiga a Zamfara
Kwamishinan ya kara da kira garesu su kara kaimi a yunkurinsu na taimaka wa kawo zaman laifya a jihar.
Ya kuma tabbatar wa mazajen samun goyon bayan gwamnati da hukumomin tsaro domin tabbatar da tsaro da aminci a jihar.
A bangarensa, Kwamishinan Tsaro ya ce gwamnatin jihar za ta ci gaba da tattaunawa da wasu hanyoyin kawo karshen matsalar tsaron.
Kwamishinan wanda ya wakilci Gwamna Bello Matawalle ya kuma nuna farin ciki da gamsuwa da nasarar da aka samu.