✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun bullo da sabon salon satar mutane

’Yan bindiga na amfani da motocin haya wajen sace mutane

Sabon salo: ’Yan bindiga na amfani da motocin sufuri wajen sace mutane a Katsina

’Yan bindigar da ke satar shanu da garkuwa da mutane a Jihar Katsina sun bullo da sabon salon sace mutane da garkuwa da su inda suke ci gaba da canja salon kai hare-harensu ta yadda yau za a ji su a nan, gobe a can.

Aminiya ta gano cewa a baya-bayan nan maharan sun fi garkuwa da mutane masu yawa a duk garin da suka kai wa hari fiye da satar dabbobi, kuma maharan sun fi sace mata da yara da tsofaffi da ba su iya guduwa, inda suke sace mutum daga goma zuwa sama.

Misali a makon nan a kauyukan Batsari da suka hada da Yasore da Biya-Ki -Kwana da ’Yar Maiwa da Dodo, maharan sun tafi da sama da mutum 20, baya ga tare hanya da suke yi a tsakanin Katsina zuwa Jibiya kusa da kauyen Kwarare inda aka ce sun tafi da fasinjojin motoci biyu cikin daji.

Wani sabon salon kuma shi ne yadda ’yan bindigar suke yawo da motocin haya yadda aka saba, suna dauki-a-jen fasinjoji a karshe su yi gaba da wanda tsautsayi ya fada masa.

An sace fasinjojin motoci biyun ne a hanyar Jibiya ba tare da fuskantar matsala daga jami’an tsaro ba, a hanyar da take da shingayen binciken ababen hawa kusan 20 a tafiyar da ba ta fi kilomita 35 zuwa 40 ba daga Katsina.

A makon jiya maharan sun je kauyen Biya-Ki-Kwana, garin da nisansa da shingen sojoji bai kai kilomita daya ba, maharan suka shiga suka yi harbe-harbe suka tafi da mata da kananan yara, ciki har da wata mai ciki, amma babu wani yunkuri da jami’an tsaron suka yi na kai dauki, inji wata majiya.

Majiyar ta ce, lokacin da aka shaida wa sojojin abin da ke faruwa, sai suka ce ba a ba su umarnin yin wani abu ba.

Irin wannan bayani inji wani mazaunin Batsari sun sha jin sa daga jami’an tsaron.

“To idan an kawo su nan don bayar da tsaro kuma aka ce sai an ba su umarni daga wani wuri can, ke nan ba su da wani amfanin zama nan.

“Wasu lokuta sai mu ga kamar da hadin bakinsu, tunda suna jin karar harbin bindiga amma sai su yi ko-in-kula.

“Ka ga yanzu, muna ji muna gani wannan hanya da ta tashi daga Batsari zuwa Jibiya ba ta biyuwa saboda masu garkuwa da kuma kisa, inda muke dan samun sauki shi ne ta bangaren ’yan sanda, to abin ya yi musu yawa, sai mu da muke taimaka musu.

“Labari ya iske mu cewa mai cikin da suka sace, ta haihu a daren da suka dauke su, amma an ce sun kawo ta wani kauye mai suna Dangeza sun sake ta tare da abin da ta haifa,” inji majiyar.

Wadansu daga cikin mutanen da Aminiya ta zanta da su a Jibiya sun nuna damuwa kan sace fasinjoji a mota biyu wanda har zuwa lokacin da aka hada wannan rahoto babu wanda zai ce ga halin da suke ciki, sai dai motocin da aka bari a bakin titi.

“Yanzu inda buhun masara ko na gero ko na siminti muka dauko daga Katsina zuwa Jibiya, sai a kwace da sunan wai za mu fita da su wajen kasa. Amma ga mutane an yi awon gaba da su shiru.

“Muna ji nan ’yan bindigar suka shigo kauyen Hirji da ke cikin Nijar, jami’an tsaronsu suka fatattako su, maimakon na nan su tarba a yi musu kofar rago, babu abin da suka yi,” inji wani da ya nemi a sakaya sunansa.

A ranar Asabar da ta gabata sai da mahara suka shiga har cikin garin Jibiya gidan wani mai suna Alhaji Bawa Wulli inda suka kashe wani yaro, suka tafi da mutum biyu, kuma har lokacin da Aminiya ta yi magana da wata majiya a garin ba bayani a kansu.

Sai dai majiyar ta ce, “A yanzu akwai wani soja da aka kai wanda in da za a samu irinsa uku da yaransu, za a iya nasara a kan miyagun yankin.

“Muddin ya ji labari zai shiga daji ya tare ko ya bi bayan miyagun.

“Ko jiya da suka shigo garin ’Yangayya ya je da mutanensa kuma kamar yadda muka samu labari, ya fatattaki maharan.

“Yanzu mu mutanen Jibiya da zarar an ce yamma ta yi, to in mutum yana Katsina sai dai ya kwana can, haka na Katsina in yana Jibiya.”

Mutanen garin Zakka da ke Karamar Hukumar Safana kuwa yabo suka yi ga jami’an tsaro, sun shaida wa Aminiya cewa, a ranar Litinin da ta gabata, maharan da suka haura mutum 30 dauke da bindigogi, sun je kauyukan ’Yarbarza da Lambo a iyakar kananan hukumomin Kurfi da Safana suka sace wata mata da yara da dabbobi, amma jami’an tsaron hadin gwiwa suka tsare su a tsakanin garin Ummadau da Kwayawa inda suka yi musayar wuta.

Majiyar ta ce ko akwai wanda ya sha daga cikin maharan, to da raunin da ba zai tashi ba zai shiga daji, amma kusan babu wanda ya haye.

Wannan labari Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina ta tabbatar da shi a wata sanarwa da Kakakinta SP Gambo Isa ya fitar, inda ya ce, an tserar da mata 17 da yara 6 da dabbobin da maharan suka sato.

Sannan an kwato babura 12, bayan kashe akalla ’yan bindiga 6 tare da raunata wadansu.

Can a Faskari da ke da sansanin sojojin Sahel Sanity, wadansu da Aminiya ta tuntuba sun ce babban kalubalen da ke damunsu shi ne tsakanin Unguwar Kindo, Mai Gora da kUnguwar Rimi.

Sun ce ya kai da rana ido na ganin ido, ake sace mutane.

Suna zargin gungun mahara na wani Bafillace mai suna Alhaji Lawal ke yin yadda suka so a yankin.

“Wato, abin sai dai a ce Allah Ya kawo karshensa,” inji wani mai suna Malam Bala.

Mai ba Gwamnan Katsina Shawara kan Tsaro, Alhaji Ibrahim Katsina ya ce, jami’an tsaro musamman sojoji abokan tafiya ne masu taimakawa a kawo karshen wannan matsala.

Ya ce yana da kyau jama’a su lura da cewa jami’an tsaron ba su da yawa.

“Wannan ya sa yanzu muke kokarin kawo jami’an tsaro na al’umma, ‘Community police.’

“Matsalar tsaron nan harka ce ta cikin gida da ya kamata a kashe ta a tsakanin juna.

“Jami’an tsaro da ake kawowa wadansu ko harshenmu ba su ji, an kawo su ne don tallafawa. Mu nemo hanyar gyara a tsakaninmu, mun san juna, mun san dalilan faruwar abin, mu zo mu gyara mu da kanmu tunda da ba haka ake ba,” inji shi.

Ya ce akwai bukatar jama’a su hada kai da jami’an tsaro wajen yaki da miyagun maimakon yin shiru ana jiran sai abin da jami’an tsaro suka yi.

Ya ce hakan ba zai haifar da da mai ido ba tunda ba su san masu aikata laifuffukan nan ba dole sai ta hanyar jama’ar da abin ke shafa za su sani.