✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun bukaci a tara musu N20m a matsayin ‘kudin fansar kai’ a kauyen Zamfara

Yaran Bello Turji ne suka bukaci a yara musu kudin don kare kauyen daga mahara

Mazauna garin Moriki da ke Jihar Zamfara, sun fara yin karo-karo domin tara Naira miliyan 20 a matsayin ‘kudin fansar kai’ da ’yan bindiga suka bukata daga wajensu.

A cewar mazauna yankin, ana bi gida-gida ne domin tattara kudin da za a kai wa ’yan ta’addan da ke karkashin Bello Turji.

Dan ta’addan da tawagarsa dai sun yi alkawarin cewa za su kare yankin daga mahara matukar aka ba su kudin kamar yadda suka bukata.

Garin Moriki dai wanda ke kan hanyar Shinkafi zuwa Kauran Namoda ya sha fama da hare-hare a baya, ciki har da na sace wani malami a wata makarantar sakandaren ’yan mata da ke garin.

Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoton, wakilinmu bai samar damar jin ta bakin Kakakin Rundunar’Yan Sandan Jihar, Mohammed Shehu ba.