✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan bindiga: NEMA ta tallafa wa ‘yan Kajuru

Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), ta raba wa ‘yan gudun hijirar da rikicin Karamar Hukumar Kajuru da ke jihar Kaduna ya shafa. Da…

Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), ta raba wa ‘yan gudun hijirar da rikicin Karamar Hukumar Kajuru da ke jihar Kaduna ya shafa.

Da yake mika tallafin, Jami’in Hukumar Mai Kula da Shiyyar Arewa Maso Yamma Imam Garki, ya ce Gwamnatin Tarayya na matukar tausaya wa mutanen da suka rasa muhallansu a irin wannan lokacin, inda ya sha alwashin taimaka wa wadanda abin ya shafa.

Ya ce NEMA ta yi kididdigar irin barna da asarar da aka yi sannan gwamnati ta bayar da tallafin kayan abinci da sauransu ga iyali 440 da abin ya shafa.

Garki, ya ce tallafin da aka bayar ya hada da kayan abinci da bokitai da kuma maganin sauro.

Babbar Sakatariyar Hukumar Ba da Agajin Gaggawa na Jihar Kaduna (SEMA) Maimunatu Abubakar, ta jaddada wa jama’ar da abin ya shafa muhimmancin zaman lafiya wanda idan babu shi, a cewarta, babu wani batun cigaba.

“Sakamakon zaman da muka gudanar da masu ruwa da tsaki kan wannan lamarin mun fahimci mutanen wannan yanki masu son zaman lafiya ne kuma suna zaune da junansu kalau kafin wannan lokacin.’

Ta kuma bukaci tallafin ya kai ga sauran bangarorin yankin da abin ya shafa, tare da shawartar jama’a da su zauna lafiya da juna.

Jami’ar ta kuma ba da tabbacin cewa gwamnati na binciken kwakwaf kan musabbabin rikice-rikicen da ke neman mai da hannun agogo baya a yankin na Kajuru.

Da yake bayyana farin cikinsa ga tallafin na Gwamnatin Tarayya, Shugaban Karamar Hukumar ta Kajuru, Cafra Caino, ya yaba wa NEMA bisa kawo agajin cikin gaggawa kamar yadda sunanta yake, don saukaka wa jama’arsa radadin da suka shiga.

Caino ya kuma tabbatar da yin adalci wajen rabon kayayyakin ga wadanda abin ya shafa gwargwadon bukatar kowane gida.