✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga na neman N50m kan mutane 10 da suka sace a Zamfara

’Yan ta'addan sun mayar da yankin Moriki saniyar tatsa a duk lokacin da suke da buƙatar kuɗi

’Yan bindiga da suka sace mutane 10 a yankin Moriki da ke Jihar Zamfara a daren ranar Laraba suna neman Naira miliyan 50 a matsayin kuɗin fansa.

Kakakin ’yan sanda a Jihar Zamfara, ASP Yazid Abubakar, ya tabbatar da hakan, amma ya ce kwamishinan rundunar ya bayar da umarnin a gaggauta kuɓutar da mutanen da aka sace su ranar Laraba da dare.

Wani mazaunin ƙauyen Moriki ya ce a baya ’yan bindiga sun matsa wa yankin da sace mutane.

“’Yan bindigar sun yi ikirarin cewa wani kwamanda a yankin ne ya kashe dabbobinsu, shi ne suka kawo hari suna shiga gida-gida su sace mutane, suka sa mana wa’adin biyan kuɗin fansa Naira miliyan 50,” in ji shi.

Ya ce ’yan bindiga suna yawan kai wa garin hari su sace mutane domin karɓar kuɗin fansa a duk lokacin da suka buƙaci kuɗi.

“Ba a jima ba suka zo suka tatse mu Naira miliyan 20 kafin su bari mu fara zuwa gonakinmu,” in ji shi.