✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga na neman N100m a kan mahaifin Shugaban Karamar Hukuma

Sun bukaci a ba su N100m kafin su saki mahaifin Shugaban Karamar Hukumar Bwari.

’Yan bindigar da suka yi garkuwa da mahaifin Shugaban Karamar Hukumar Bwari da ke Abuja, John Shekwogaza, sun bukaci Naira miliyan 100 a matsayin kudin fansa.

A ranar Talata Aminiya ta rawaito yadda ’yan bindigar suka shiga kauyen Tokulo, a Abuja suka yi garkuwa da mahaifin Shugaban Karamar Hukumar da kuma wasu mata biyu.

Iyalan dattijon sun bayyana cewa “A yammacin ranar Talata ne suka kira mu a waya suna bukatar N100m kafin su sake shi.”

Sun ce tun bayan sace mahaifin nasu sun kasa samun sukuni, amma suna rokon su kan su rage kudin da suke bukata.

Kakakin ’yan sandan Abuja, ASP Maryam Yusuf, ba ta dauki waya ko mayar da sakon wakilinmu bare mu ji ta bakinta kan lamarin.