✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga na barazanar kashe daliban Jami’ar Gusau nan da kwana 7

Iyayen daliban Jami’ar Tarayya ta Gusau da ke Jihar Zamfara, sun roki gwamnati ta gaggauta ceto ’ya’yan nasu sakamkon barazanar kashe daliban cikin kwana bakwai…

Iyayen daliban Jami’ar Tarayya ta Gusau da ke Jihar Zamfara, sun roki gwamnati ta gaggauta ceto ’ya’yan nasu sakamkon barazanar kashe daliban cikin kwana bakwai da ’yan bindigar suka yi.

Iyayen sun ya kamata gwamnatin ta tattauna da ’yan bindigar, kamar yadda ta yi da ta’adda a baya, musamman a lokacin ganiyar rikicin Boko Haram.

Sun yi wannan rokon ne a bayan barazanar da ’yan bindigan suka yi ranar Laraba cewa za su kashe daliban idan ba a biya musu bukatunsu ba.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da wasu majiyoyi suke cewa, ’yan bindiga sun nada sabon shugaba, wanda shi ne a halin yanzu yake rike da daliban kuma yake barazanar fara kashe su idan ba a biya musu bukatunsu ba — ciki har da sakin wasu kwamandojinsu da ke tsare a hannun jami’an tsaro.

Tun lokacin da aka sace daliban, Ofishin Mashawarcin Shugaban Kasa kan Tsaro (ONSA),  ke jagorantar tattaunawa da Hedikwatar Tsaro da Hukumar DSS kan yadda za a kubutar da daliban.

Iyayen daliban sun shaida wa wakilanmu cewa sun samu labarin sakonnin sauti barazanar kashe wasu daga cikin daliban da ’yan bindiga suka fitar.

Aminiya ta samu sakonnin wasu wadanda suka ce yaran jagoran ’yan bindiga, marigayi Ali Kachalla ne suka saki bidiyo a WhatsApp, suna neman gwamnati da jami’an tsaro su saki abokansu da ke tsare a matsayin sharadin kare rayukan daliban da ke hannunsu.

A kwanakin bayan ne dai Aminiya ta ruwaito cewa sojoji kashe Ali Kachalla a yayin wani samame da rundunar sojojin saman Najeriya ta kai a Jihar Neja.

Daga bisani Hedikwatar tsaro (DHQ) ta tabbatar da kashe Ali Kachalla, a ranar 11 ga watan Disamba a karamar hukumar Munya ta jihar tare da yawancin daga cikin kwamnadoji da yaransa.

Ali Kachalla ne ya sace dalibai sama da 50, akasarinsu mata a Jami’ar FUGUS a ranar 21 ga Satumba, 2023.

Kashe Ali Kachalla — hatsabibin dan bindiga ne da ya tafka ta’asa a jihohin Sokkwato, Zamfara, Katsina, Neja, Kaduna da dai sauransu — ya kawo cikas ga abokan cin mushensa, wadanda yanzu suke barazanar kashe wasu daga cikin daliban jami’ar da ke hannunsu.

Tun da aka kashe Ali Kachalla iyalai da ’yan uwan daliban  ke ta fargaba game da makomarsu.

A wani sakon sauti ta WhatsApp, an ji wani mai magana da daya daga cikin shugabannin ’yan bindigar  na rokon su su janye baganar kashe daliban, inda ya ce ana ci gaba da sasantawa.

A cikin sautin da muka yi bita, an ji shugaban ’yan bindigar na cewa sun gaji da sayar da shanunsu su ciyar da ’yan matan.

“Mun gaji da ciyar da su. Ya kamata ku sansar da wadanda abin ya shafa. Mun ba su kwanaki bakwai su sako mutanenmu.”

Da yake mayar da martani, mai magana da sun ya ce, “Don Allah kada ku da ku kashe ’yan matan saboda ba laifin su  ba ne.”

Amma shugaban ’yan fashin ya ce, “To ku gaya wa gwamnati ta sako mutanenmu. Sun dade suna tsare mutanenmu a gidan yari”.

Sannan ya ce: “Mun ji cewa (jami’an tsaro) na son yin amfani da karfi soja wajen kwato daliban. To, kafin su yi amfani da karfi, ku gaya musu cewa za mu fara yanka akalla uku daga cikin ’yan matan duniya ta ga hotunansu.

“Idan suna ganin suna da karfin kwato ’yan matan, me ya sa ba su tunkare mu ba lokacin da muka je sace su tun farko? Mun ji duk abin da suke faɗa saboda muna sauraron rediyo. Dole ne su saki mambobinmu kafin mu ma mu sako wadanda ke hannunmu.

A wani faifan faifan sauti, maganar ya roki ’yan bindigar da su kara hakuri: “Na dade rabona da magana da masu shiga tsakani, amma zan yi iya kokarina na gana da su da kuma tabbatar da magance matsalar.”

Shugaban ’yan bindair ya ce, “Kai ma ka san cewa su (gwamnati) ba kaifi daya ba ne, za su faɗi wani abu yau, gobe su canza.”

Amma mai magana da su ya ce, “ina so in tabbatar muku cewa bisa tattaunawar da muka yi, wadanda ke da alhakin sun yi alkawarin cewa za a yi musanyarda daliban.”

Daga cikin kwamandojin da ’yan bindigar ke son a sako akwai wani kanen Ali Kachalla mai suna Ibrahim, duk da cewa akwai mambobinsu sama da 50 a tsare a cewarsu.

Daya daga cikin majiyoyin mu ya ce ko da yake wasu daga cikin ’yan fashin da aka kama suna raye bai da tabbacin sauran.

Majiyar ta ci gaba da cewa, “An kama wasu daga cikin ’yan bindigar ne a lokacin da suke musayar wuta kuma sun samu raunuka. Don haka, ba za ku iya sanin ko suna raye ko a’a ba.”

 

Sagir Kano Saleh, Hamza Idris, Idowu Isamotu (Abuja) & Yusha’u Ibrahim (Sakkwato)