A wani yunkuri na karya lagon ’yan bindiga, Gwamnatin Jihar Sakkwato ta kafa dokar haramta sayar da man fetur a jarkoki a fadin jihar nan take.
Sabuwar dokar da Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya yi ta rufe hanyar Illela zuwa Isa da kuma sayar da dabbobi a kananan hukumomin da ke fama da matsalar tsaro a jihar sai a bin da hali ya yi.
Dokar ta haramta goyon mutum fiye da daya a kan babur mai kafa biyu ko goyon mutum fiye da biyu a babur mai kafa uku, tare da takaita amfani da babura a Jihar.
“Dokar ta fara aiki nan take daga Laraba, 1 ga Satumba, 2021,” kamar Kwamishinan Yada Labaran Jihar Sakkwato, Isa Bajini Galadanci, ya bayyana a madadin gwamnan.
“An haramta baburan haya aiki daga 10:00 na dare zuwa 6.00 na safe a garin Sakkwato; amma haramcin zai yi aiki ne daga 6.00 yamma zuwa 6.00 na safe a kananan hukumomin Gada, Goronyo, Gudu, Gwadabawa, Illela, Isa, Kebbe, Sabon Birni, Rabah, Tambuwal, Tangaza, Tureta da Wurno.”
“Ayyanannun gidajen mai kadai aka amince su sayar wa masu ababen hawa da mai na fiye da N5,000 a kananan hukumomin.
“An kuma rufe hanyar Isa zuwa Marnona ga masu ababen hawa har sai abin da hali ya yi, saboda haka matafiya da ke bin hanyar za su koma bi ta hanyar Goronyo zuwa Sabon Birni.
“Manyan motoci da sauran motocin da ke harkar daukar ice daga dazuka ma an haramta ayyukansu a jihar.
“An kuma haramta jigilar dabbobi a manyan motoci a kananan hukumomin Gada, Goronyo, Gudu, Illela, Isa, Kebbe, Sabon Birni, Shagari, Rabah, Tambuwal, Tangaza, Tureta da kuma Wurno,” inji shi.
Gwamna Tambuwal ya kuma haramta sayar da babura na hannu a kasuwannin kananan hukumomin da kuma kasuwannin Achida, Gande da Gwadabawa.
Da yake kira ga mutanen jihar da su kasance masu biyayya ga sabuwar dokar, Tambuwal ya ce an kafa ta ne bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki da suka dace a Jihar Sakkwato da nufin tabbatar da tsaro da walwalar jama’a da kuma ci gaban harkokin tattalin arziki.