’Yan sanda da mafarautan Ali Kwara sun far wa bata-garin ne a matsaysin martani kan kisan gilla da miyagun suka yi wasu mutum takwas, ciki har da basaraken kauyen Kada Gamji da ke a karamar hukumar.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Bauchi, Auwal Musa Muhammad, ya sanar ranar Laraba a Ningi cewa a makonni biyu da suka gabata, ’yan bindiga sun kai hari a kauyukan Iyayi, Kayadda, Gamji da Bukutumbe, inda suka harbi mutum hudu, suka kashe wani dan banga a Bukutumbe.
- Kisan dan aiki: Kotu ta tsare matar aure a gidan yari
- ’Yan bindiga sun sace mutane ana tsaka da cin kasuwa a Taraba
Daga nan kuma suka tsallaka Jihar Jigawa, inda suka yi garkuwa da mata biyu na Shugaban Karaman Hukumar Kiyawa.
Kwamishinan ’yan sandan ya ce bayan kisan gillar da aka yi wa mutane takwas a Ningi a watan Yuli ne rundunar ta tada wata tawagar jami’an tsaro na sirri da hadin gwiwar mafauta yaran Ali Kwara.
CP Muhammad ya bayyana cewa rundunar hadin guiwar ta yi artabu da ’yan bindigar ne a maboyarsu da sanyin asubahin a ranar 26 ga Disamba, 2023, inda suka kashe shida daga cikinsu.
A cewarsa, jami’an sun kwato bindiga kirar AK47 guda biyu, harsashai 55, kwanson harsasai, kudi Naira miliyan 4.5, mota kirar Golf 3, sabbin layukan waya guda bakwai, da wayoyi guda shida da sauransu daga hannun ’yan bindigar.