✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga 31 sun shiga hannu a Nasarawa

Kwamishinan ya ce za su miƙa su kotu da zarar sun kammala bincike.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Nasarawa ta kama wasu mutum 11 da ake zargin masu garkuwa da mutane ne da suka addabi mazauna ƙauyen Nunku da ke ƙaramar hukumar Akwanga, Masaka da kuma ƙaramar hukumar Karu da sauran ƙananan hukumomin jihar.

Rundunar ta kuma kama wasu mutum 13 da laifin aikata fashi da makami a ƙaramar hukumar Karu.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, Mista Shehu Umar-Nadada, yayin da yake gabatar da waɗanda ake zargin a garin Lafiya, ya ce an kama ɗaya daga cikin waɗanda da ake nema ruwa a jallo a kan satar mutane a ƙananan hukumomin Doma, Lafia da Keana na jihar.

A cewarsa, “A ranar 28 ga watan Yuni 2024 da misalin ƙarfe 10:30 na dare, jami’an ’yan sandan yankin Masaka suka kai samame tare da kama Ahmadu Ibrahim ( mai shekara 20), Mohammed Abubakar (mai shekara 30) da Jibrin Ahmadu (mai shekara 30).”

Ya ƙara da cewa waɗanda ake zargin sun amsa cewar suna garkuwa da mutane a yankunan Assakio, Gallo da Mankwar, duk a yankin Lafia ta Gabas.

Kwamishinan ya ce da zarar sun kammala bincike a kansu za su gurfanar da su a gaban kotu.