✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindida sun kashe mutum 10 a masallaci a Katsina

Maharan sun bude wa mutane wuta yayin da suke sallar Magariba.

’Yan bindiga ne sun kai farmaki garin Yasore da ke Karamar Hukumar Batsari ta Jihar Katsina, inda suka kashe mutum 10 da suke yin sallah a cikin masallaci tare da raunata wasu 11.

’Yan bindigar sun kashen mutum 10 din ne ta hanyar bude musu wuta a yayin da mutanen suke tsaka da yin sallar Magariba a masallacin.

Aminiya ta gano cewa an yi jana’izar wadanda suka rasun a ranar Laraba, wadanda suka ji rauni kuma aka garzaya da su zuwa Babban Asibitin garin Batsari inda ake ba su kulawa.

Aminiya, ta gano cewa dandazon ’yan bindigar da suka kai wa garin farmaki sun fito ne daga dajin Birnin Gwari da ke Jihar Kaduna.

Maharan sun yi wa garin dirar mikiya ne da misalin karfe 6 na yammacin ranar Talata, sannan suka kone gidaje da dama.

Wani mazaunin yankin da ya bukaci a sakaya sunansa ya ce sun kai harin ne duk da atisayen da dakarun soji ke yi na dakile ’yan bindiga a jihar.

“Mun ga amfanin atisayen da dakarun soji ke yi, don yana haifar da sakamako mai kyau, amma duk da haka manoma na shan wahala wajen girbe amfanin gonar da suka noma,” a cewarsa.

Ya kara da cewa mutanen yankin da suka tsira daga harin sun yi kaura zuwa cikin garin Batsari don neman mafaka.

Kakakin ’yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya tabbatar da faruwar lamarin.

“’Yan bindigar sun kai harin ramuwar gayya ne. An kashe mutum 10 yayin da wasu 11 suka jikkata.

“Kwanan nan ’yan sa-kai sun shiga cikin gari suna kashe Fulani, saboda haka ’yan bindigar sun je wurin ne don yin ramuwar gayya.

“Duk wani daga cikin ’yan sa-kai da aka kama daga yanzu za a dauki shi a matsayin dan bindiga,” inji shi.