✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun sace dalibai 10 a Kaduna

’Yan bindiga sun sace dalibai 10 a Kaduna

’Yan bindiga sun sace dalibai akalla 10 a Karamar Hukumar Kachia ta Jihar Kaduna.

Gwamnatin Jihar ce dai ta tabbatar da labarin, inda ta ce ta samu rahoton hakan ne daga jami’an tsaro kan satar daliban.

Hakan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Kwamishinan Tsaro da Al’amuran Cikin Gida na Jihar, Samuel Aruwan, ya fitar ranar Talata.

Ya ce binciken farko ya nuna musu cewa an sace daliban ne a makarantar Sakandiren Gwamnati da ke Awon, a ranar Litinin.

Aruwan, ya ce kodayake har yanzu ba a kai ga tantance wurin da maharan suka kai daliban ba, amma suna kokarin tattara bayanai don gano ko lamarin ya faru ne cikin makarantar ko kuma a wajenta.

Kwamishinan ya yi alkawarin bayar da sanarwa a kai da zarar sun sami cikakkun bayanai.