✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan banga sun kwato mutum 12 a hannun ’yan bindiga a Zariya

’Yan bindiga sun kai hari kusa da gidan talabijin na NTA da ke Zaariya

’Yan bindiga sun kai hari a bayan gidan Talabijin na Kasa (NTA) da ke Dakace a Zariya inda suka shiga gidan wani mutum za su sace shi.

Wani mazaunin garin da ya bukaci a boye sunansa ya shaida wa wakilinmu cewa maharan sun shiga gidan ne da misalin karfe 1.30 na daren Asabar, amma ba su sami maigidan ba, ya riga ya tsere da ya ji motsinsu.

Yace duk da ba su same shi ba, ’yan bindigan sun yi awon gaba da matansa biyu da ’ya’ya 10.

A cewarsa, nan da nan aka sanar da ’yan banga suka fito suka bi su.

“Bayan sun yi ba-ta-kashi, ’yan bangar sun sami nasarar kwato dukkanin wadanda ’yan bindigar suka sace, maharan kuma suka ranta a na kare.

Aminiya ta gano cewa harin ya sanya mazauna yankin fargaba, ganin shi ne na farko yankin na Dagace.

Binciken Aminiya ya gano cewa ’yan bindigar da ke kai hare-hare a yankunan Zariya suna gudanar da ayyukansu ne ta yankunan da ke Yammacin garin, sa’ilin da a karon farkon aka ji bullarsu ta Gabashin Zariya.

Duk da kokarin jin ta bakin kakakin ’yan sandan Jihar Kaduna, ASP Muhammad Jalige, ta hanyar kiran waya, amma bai dauki wayar ba.

%d bloggers like this: