✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan banga sun kama ɓarayin shanu a Neja

Ɓarayin sun shiga hannu ne bayan sun shanun satar kasuwar da nufin sayarwa.

’Yan banga sun kama wasu mutum biyu da ake zargin ɓarayin shanu ne a kasuwar Lambata da ke Jihar Neja.

Wani mazaunin yankin Gawu, Usman Aliyu, ya ce waɗanda ake zargin sun sace shanun ne a wata rugar Fulani da ke ƙauyen Tungan Usman a gundumar Gawu a ƙaramar hukumar Abaji da ke Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Ya ce, “Bayan makiyayin ya gano cewa shanunsa guda biyu sun ɓata a ranar Larabar da ta gabata, sai ya sanar da shugaban Fulanin da ke kula da kasuwar.

“Waɗanda ake zargin sun kawo shanun kasuwa, domin su sayar da su a ranar Alhamis.”

Aminiya ta kuma samu labarin cewa a ranar Asabar, wani makiyayi ya harbe wani wani ɓarawl a rugar Fulani da ke ƙauyen Mayaki.

Kakakin rundunar ’yan sandan babban birnin tarayya Abuja, SP Josephine Adeh, ba ta ce uffan ba kan lamarin ba.