✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan banga sun harbe mace mai garkuwa da mutane, sun kama wasu 12     

’Yan banga a Jihar Kaduna tare da hadin gwiwar wasu matasa sun harbe wata mata da ake zargin mai garkuwa da mutane ce tare da…

’Yan banga a Jihar Kaduna tare da hadin gwiwar wasu matasa sun harbe wata mata da ake zargin mai garkuwa da mutane ce tare da kama wasu 12 a Karamar Hukumar Lere da ke jihar.

Aminiya ta samu rahoton cewa, ’yan bangar sun kai farmaki a mabyar masu garkuwa da mutane da ke yankin Garun Kurama a yankin Mariri da ke karamar hukumar a ranar Talata.

Wani shugaban al’ummar da aka sakaya sunansa saboda dalilan tsaro, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce ’yan bindiga na addabar al’ummar yankin.

“Gaskiya ne an kama wadanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne a ranar Talata. Muna fama da hare-harensu a wannan yanki,” in ji shi.

Hakazalika, wani dan banga da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce an kashe matar da ake zargin ta ne a yayin samamen da misalin karfe 3 na rana.

“Mun kama masu garkuwa da mutane 13 a maboyarsu tare da wasu matasa; Mun lalata sansaninsu kuma an kashe mace daya da ake zargi a nan take,” in ji shi.

A cewarsa, an mika wadanda aka kama ga ’yan sanda.

Amma da aka tuntubi Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ’Yan Sandan jihar, DSP Mohammed Jalige, ya yi alkawarin jin yadda lamarin ya faru domin tuntubar wakilinmu.

Sai dai har yanzu bai yi hakan ba har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto.