✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan Arewa sun ƙi amfani da damar da suka samu na shugabancin Najeriya – Dogara

Ya kamata ’yan Arewa su yi watsi da yunƙurin ɗora wa Shugaba Tinubu alhakin halin da yankin Arewa ke ciki a halin yanzu.

Tsohon Shugaban Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara, ya danganta koma-baya da ake samu yankin Arewa a halin yanzu ga shugabanni ‘yan siyasar yankin ne.

Ya kuma buƙaci ‘yan Najeriya da su marawa shugaba Bola Tinubu baya wajen kawo sauyi ga al’ummar ƙasar ta hanyar ƙudurorin gyaran haraji da ke jiran amincewar majalisar dokokin ƙasar a halin yanzu.

Dogara ya bayyana hakan ne a wani taron jagororin kiristoci ‘yan yankin Arewaci, inda ya ce shugabannin yankin ba su yi amfani da damar da suka samu ba na kusan shekara 40, wanda hakan ne ya jefa yankin cikin talauci da rashin aikin yi.

A cewar Dogara, ya kamata ’yan Arewa su yi watsi da yunƙurin ɗora wa Shugaba Tinubu alhakin halin da yankin Arewa ke ciki a halin yanzu. Ya kuma jaddada buƙatar a haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen tallafawa ƙudirin gyaran haraji, wanda ya ce an tsara su ne domin kawo sauyi ga Arewa da Najeriya baki ɗaya.

“Dukkanmu ’yan Arewa ne, kuma ya kamata a bayyana cewa ba Shugaba Tinubu ko yankin Kudu ba ne matsalarmu ba ce. Ba su zo su cuci yankin Arewa ba. Wannan ba ya cikin tambayar. Wasu suna iƙirarin cewa Yarabawa suna samun muƙamai, amma mu yi tunani. Mun yi mulkin ƙasar nan sama da shekara 40 a lokacin da ’yan Arewa ke mulki. Me muka cimma? Arewa ta kasance a yadda take,” in ji Dogara.