✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan Arewa sun yi gangamin wayar da kan jama’a a Shagamu

Shugabannin ’yan Arewa mazauna Jihar Ogun a ƙarƙashin jam’iyar APC, sun shirya taron wayar wa junansu a garin Shagamu. Taron, wanda ya samu halartar shugabannin…

Shugabannin ’yan Arewa mazauna Jihar Ogun a ƙarƙashin jam’iyar APC, sun shirya taron wayar wa junansu a garin Shagamu.

Taron, wanda ya samu halartar shugabannin ’yan Arewa daga sassan ƙananan hukumomin jihar, ya hada da jama’a da dama da suka halarci taron. Alhaji Usman Shehu Samfan, shugaban ƙungiyar ’yan Arewa a jam’iyar APC na Jihar Ogun, shi ne ya jagoranci taron. Ya shaida wa Aminiya cewa sun shirya taron ne domin ganawa da al’ummar Arewa mazauna jihar tare da fadakar da su muhimmancin zaman lafiya, ganin yadda ƙurar da ta taso a yankin Kudu maso gabas. 

“Don haka muka tara jama’armu muka yi masu tanbihin zaman lafiya da haƙuri da juna, mun ja hankalinsu a kan su rika shiga ana damawa da su ta fuskar siyasa, domin a haka ne za su sami damar magance da yawa daga cikin matsalolin da ke addabarsu,” inji shi.

Samfan ya yaba wa gwamnan jihar a yunƙurinsa na sake ginin jihar, tare da sauya mata fasali. Ya ce ko ba komai zaman lafiyar da aka samu a jihar abin a yaba wa gwamna Amusu ne, domin sai da zaman lafiya ne ake samun ci gaba a kowane fanni. Sai dai ya yi ƙorafin cewa ’yan Arewa ba su da wani wakilci na a zo a gani a gwamnatin jihar, duk da irin gudunmawar da suke bayarwa. 

“Akwai garuruwa da muke da tarin jama’a kamar garuruwan Ifo da Ijebu Ode da Shagamu da Ibafo da Abeokuta da makamanta wannan; duk in ka je za ka ga tarin ’yan Arewa. Kamata ya yi a ce muna da wakilci koda a ƙananan hukuma ne da wasu gurabe a matakin tarayya. Amma za mu miƙa wa gwamnati kukanmu a siyasance kuma muna kyautata zaton za su share mana hawayenmu,” inji shi.

A nata ɓangaren, shugabar matan Arewa ta jihar Ogun a kungiyar, Hajiya Asabe Sahabi, kira ta yi ga matan Arewa na jihar da kada su bari a bar su a baya a siyasance, inda ta shawarce su da su rika fitowa ana damawa da su.

Shugabannin taron sun jadadda wa mahalarta taron muhinmancin katin zabe, inda suka ba da shawarwari na musamman ga mutanen da suka sauya mazauninsu da ma waɗanda nasu katin zaɓen ya ɓata da kuma waɗanda sai a yanzu ne suka cika shekarun yin rijista, suka ce za su tabbatar sun sami tasiri a zaɓuka masu zuwa nan gaba.

A ƙarshe an rufe taron da yi wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari addu’ar samun ƙarin ƙoshin lafiya da nasara a harkokin jagorancin da yake yi wa Najeriya.