✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan acaba sun sake tayar da yamutsi a Abuja

An sake kwatanta irin tashin-tashinar da ta faru a kasuwar Dei-Dei da ke Abuja.

Mako biyu bayan wata arangama tsakanin ’yan kasuwa da ’yan acaba a kasuwar Dei-Dei, wani lamari makamancin haka ya sake afkuwa a Abuja.

Sabon rikicin ya samo asali ne bayan wani direban mota ya murkushe wasu masu babura biyu har lahira a kusa da rukunin gidaje na Global Dakwo da ke unguwar Galadimawa da misalin karfe 1:30 na ranar Lahadi.

Rahotanni sun ce domin kauce wa fushin ’yan acaba, direban motar ya tsere zuwa cikin rukunin gidajen, ’yan acaban kuma suka bi bayansa don daukar fansa.

Wasu rahotanni na cewa fusatattun ’yan acaban sun lalata kadarori tare da kone wasu gidaje.

Amma kakakin ’yan sandan Abuja, DSP Josephine Adeh, ta ce babu wani gida da aka kona a yayin hatsaniyar.

“Ya zama dole mu tsage gaskiya daga labaran da ake yadawa, babu wani gida da aka kone,” in ji ta.

Ta ce ’yan acaban sun kai hari gidan da direbn ya shiga don neman mafaka, amma an samar da zaman lafiya bayan ’yan sanda sun kai dauki wajen da lamarin ya faru.

Ta ce kwamishinan ’yan sandan Abuja, Babaji Sunday, ya je wurin da lamarin ya faru don tabbatar da zaman lafiya a yankin.

Adeh ta yi alkawarin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi al’ummar Abuja ta kuma yi kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu, su ci gaba da gudanar da harkokinsu ba tare da fargabar tsangwama ko cin zarafi ba.

%d bloggers like this: