✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yakin Tigray ya lakume sama da rayuka 600,000 a Habasha —Obasanjo

Wadanda suka jikkata ba a san adadinsu ba bare kuma wadanda suka rasa matsugunansu.

Sama da mutum 600,000 sun mutu a yakin da aka shafe shekaru biyu ana yi tsakanin Gwamnatin Habasha da ’yan tawayen Tigray na kasar.

Mai shiga tsakani na Kungiyar Tarayyar Afirka, kuma tsohon Shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ne ya bayyana wa jaridar Financial Times a ranar Lahadi.

Obasanjo ya tabbatarwa da jaridar ta FT, cewa yakin ya yi mummunar barna a kasar, musamman yankin da aka gwabza a ciki.

Bayanai sun ce abu ne mai matukar wuya a iya tantance adadin wadanda suka mutu a yakin na Tigray.

Ko a dan tsakanin nan masu bincike sun ce dubun-dubatar mutanen da ba su san hawa ba su san sauka ba suka mutu a yakin.

A ranar Lahadin karshen mako jaridar FT ta ambato Shugaban Hukumar Kare Hakkin Dan Adam ta kasar Daniel Bekele na cewa ya kamata a sake bincike kan adadin da dukkan bangarorin biyu suka bayar na wadanda suka mutu.

“Ta yiwu wadanda suka mutu sun zarce 600,000 wadanda suka jikkata ba a san adadinsu ba bare kuma wadanda suka rasa matsugunansu.”

A watan Nuwambar 2020 ne Firaiministan Habasha Abiy Ahmed, ya bai wa sojin kasar umarnin kaddamar da hari kan ’yan tawayen ’yantar da yankin Tigray.

Hakan ya biyo bayan kai hari da ’yan tawayen suka yi kan sansanin sojin Habasha.