Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, a ranar Litinin ya ce kasarsa ba za ta amince da duk wani matakin tsagaita wuta tsakaninta da Hamas ba, har sai ta ga bayanta.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito Netanyahu na cewa a kowanne yaki, a kan samu fararen hular da ba su ji ba ba su gani ba da suke shan wahala, inda ya ce fadan da suke yi da Hamas a Zirin Gaza fafutuka ce tsakanin “wayewa da gidadanci”.
- An shiga rudani bayan rushe fadar basarake a Abuja
- Boko Haram na iya shafe Najeriya idan ba a tashi tsaye ba — Zulum
A yayin wani taron manema labarai a birnin Tel Aviv, Ministan Tsaron Firaministan, Yoav Gallanta, da Ministan Tsare-tsare, Ron Dermer, sun yi wa ’yan jarida bayani.
Ron ya ce alakar kasarsa da Amurka wajen yakar Hamas ita ce irinta mafi girma a tarihi, sannan ya ce alakarsu da kasar Rasha ta shiga tsaka mai wuya.
Shi kuma Yoav ya ce a daukacin Zirin Gaza da suka mamaye, sojojin Isra’ila ne kawai aka amince su yi amfani da karfi.
Netanyahu ya kuma ce, “lokaci ya yi da za mu yanke shawarar ko za mu yi fada saboda gobenmu mai cike da haske, ko kuma za mu mika wuya ga ’yan kama-karya.
“Kamar yadda Amurka ba za ta yarda da tsagaita wuta ga wadanda suka kai mata harin 11 ga watan Satumban 2001 ba, haka ita ma Isra’ila ba za ta taɓa saurara wa wadanda suka kai mata harin ranar 7 ga watan Oktoba ba.
“Kiran a tsagaita wuta kamar kira ne ga Isra’ila ta mika wuya ga Hamas, ta’addanci da kuma duhun kai. Hakan ba zai taba faruwa ba.”
Ita ma Amurka, ta bakin Kakakin Majalisar Tsaron Kasar, John Kirby, ta ce ba ta amince da batun tsagaita wutar ba a matsayin mafita.
“Abin da muka yi amanna da shi shi ne duk wani mataki na tsagaita wuta yanzu, Hamas kawai zai amfana,” in ji John.
Hare-haren Isra’ila dai sun sanadin kashe sama da Falasdinawa 8,000 tun ranar 7 ga watan Oktoba, kuma galibinsu ƙananan yara ne.
Sai dai ana fargabar adadin ma zai iya karuwa yayin da Isra’ila take kokarin fadada hare-haren ta hanyar kaddamar da wasu ta kasa a Zirin na Gaza.