Gwamnatin Gombe ta yi alkawarin hada kai da kungiyar farar hula ta CS-SUNN mai rajin samar da lafiyayyen abinci domin magance matsalar rashin abinci mai gina jiki a jihar, musamman ga kananan yara.
Sakataren gwamnatin jihar, Farfesa Abubakar Ibrahim Njodi, ya yi wannan alkawarin ne a lokacin wata ziyara da kungiyar CS-SUNN din ta kai ofishinsa domin tattaunawa kan matsalar karancin abinci mai gina jiki.
Njodi ya ce ziyarar ta zo a kan gaba, domin ma’aikatar kimiyya, fasaha da kirkire-kirkire, ta ya hada masana da masu ruwa da tsaki wajen samar da hanyoyin samar da abinci a cikin gida don magance matsalar rashin abinci mai gina jiki, wanda ake rabawa a cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko.
Ya jaddada cewa abinci mai gina jiki shi ne babban abin da gwamnati ta sa gaba, domin jihar Gombe ce ke baya a cikin jihohin kasar nan a wannan fanni.
- Dalilai uku da ke janyo rikici tsakanin ’yan siyasa da sarakuna
- Gwamnati za ta jingine harajin shigo da shinkafa da alkama
Sai dai tare da tallafin CS-SUNN, gwamnati ta himmatu wajen magance matsalar rashin abinci mai gina jiki a jihar.
Njodi, ya bai wa tawagar CS-SUNN tabbacin hadin gwiwar gwamnati, lura da muhimmiyar rawar da suke takawa wajen yaki da rashin abinci mai gina jiki.
A nata jawabin, Ko’odinetan CS-SUNN na jihar, Comfort Mukollo, ta bukaci gwamnati da ta kara kason kudi na kasafin abinci mai gina jiki tare da tsawaita hutun haihuwa ga mata masu shayarwa domin tabbatar da samun isasshen lokacin shayar da ’ya’yansu.
Wannan hadin gwiwar na da nufin inganta abinci mai gina jiki ga yara a jihar Gombe da kuma rage yawaitar rashin abinci mai gina jiki.