Shugabanin kabilun Tibi da Fulani sun amince su dakatar da kashe-kashe da ke aukuwa a tsakanin bangarorin a Jihar Taraba.
An yi sulhun ne bayan taron da shugabanin Tibi da Fulani suka gudanar a garin Jalingo a ranar Lahadi inda suka kulla yarjejeniyar ajiye makamai su zauna lafiya a tsakaninsu.
- Gobarar tankar mai ta jikkata mutum 64 a Kano
- An tsige Hakimin Kankara saboda hada baki da ’yan bindiga
Yarjejeniyar zaman lafiyar, wadda Sarkin Fulanin Bali, Alhaji Adamu Abacha da Shugaban Tibi na Bali, Mista David Zaki Gbaa suka sanya wa hannu ta amince da cewa duk wadanda yakin ya raba da garuruwansu su koma gidajensu.
An kuma amince a kafa kwamiti mai mutane 15 daga kabilun biyu domin wayar da kan jama’arsu kan muhimancin zaman lafiya.
Sun kuma amince cewa bangarorin za su sa ido domin hana masu hura wutar fitina a tsakanin Tibi da Fulani su sake haddasa wata rigima a tsakaninsu a nan gaba.