Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya bayyana cewa, rashin bude jami’o’i a dalilin yajin aiki ya sanya dalibai zama ba tare da yin komai ba a halin yanzu, saboda haka akwai bukatar tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin kawo karshen yajin aikin.
Mai Martaba Alhaji Sa’ad Abubakar ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin taron da kungiyar tsofaffin daliban Kwalejin Barewa ke gudanarwa duk shekara a Kano.
- ‘Ya kamata Sarkin Musulmi ya hana yin kayan aure’
- ‘Ciyar da daliban Kano kan lakume N4bn duk shekara’
- Shirin Ilimi Kyauta kuma Tilas a Jihar Kano: Sai kowa ya ba da goyon baya
Sarkin musulmin ya bukaci kungiyar tsofaffin daliban ta mayar da hankali wajen tattaunawa tare da sanya masu ruwa da tsaki a kan kawo karshen yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’I ta ASSU ke yi a kasar nan na tsawon watanni 7 zuwa 8.
Yayin da yake gabatar da jawabi, Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje Wanda mataimakinsa Nasir Yusif Gawuna ya wakilta, ya ja hankalin kungiyar a kan ta fito da hanyoyi da za a ciyar da kasar nan gaba musamman ta fannin ilimi, inda ya buga misali da yadda Gwamnatin Kano ta dauki nauyin bai wa al’umma ilimi kyauta.
Taron ya samu albarkacin manyan mutane ciki har da Sarkin Kano Aminu Ado Bayero, wanda shi ma yayin jawabinsa ya yi kira ga gwamnatin tarayya da kuma kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) a kan sasanci domin ci gaban ilimi a Najeriya.
Masu sharhi a kan al’amuran yau da kullum na ganin cewa yajin aikin ya taka muhimmiyar rawa yayin zanga-zangar #EndSARS da aka yi.