Kungiyar ma’aikatan wutar lantarki ta kasa za ta bi sahun takwararta kwadago ta Najeriya (NLC), domin nuna adawarsu kan yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ke yi.
Wata sanarwa mai dauke da sa hannun Babban Sakataren kungiyar, Joe Ajaero, ta bukaci dukkan mambobin kungiyar su shiga zanga-zangar.
- Matsalar tsaro: NNPP ta bukaci Buhari ya yi murabus
- LABARAN AMINIYA: Barazanar Tsaro Ta Janyo Rufe Makarantun FGC A Abuja
Aminiya ta rawaito cewa, a makon da ya gabata ne NLC ta sanar da shirinta na gudanar da zanga-zangar hadin gwiwa da sauran kungiyoyin kwadago domin nuna adawa da kuma mara wa ASUU baya kan yajin aikin da malaman jami’o’in kasar ke yi.
“An umurci dukkan mambobin kungiyar da su fito su shiga cikin zanga-zangar hadin guiwa tsakanin NLC/ASUU don nuna rashin amincewarsu da ci gaba da rufe manyan makarantun kasar nan a ranar 26/27 ga Yuli, 2022.
“Ana bukatar yin aiki tare da shugabannin Majalisar Zartarwa ta Jiha (SEC) a cikin jihohinku daban-daban don samun nasarar gudanar da zanga-zangar.”
Idan ba a manta kungiyar kwadago ta kasa ta lashi takobin shiga zanga-zanga a fadin kasar nan, don mara wa ASUU baya kam takaddamar yajin aikin da ke tsakaninta da gwamnatin tarayya.
Tun a ranar 14 ga watan Fabrairun 2022 ne ASUU ta tsunduma yajin aiki, lamarin da ya janyo kulle daukacin jami’o’in kasar nan wanda kuma hakan ya kawo tsaiko a karatun dalibai.