✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yajin aiki: Zauren Hadin Kan Malamai na so gwamnatin Kano ta sasanta da ’yan A Daidaita Sahu

Kiran na zuwa ne a daidai lokacin da yajin aikin direbobin ya shiga yini na uku.

Zauren Hadin Kan Malamai da Kungiyoyin Addinin Musulunci a Jihar Kano ya yi kira ga gwamnatin Jihar da kungiyar direbobin babur mai kafa uku da aka fi sani da A Daidaita Sahu da su sasanta tsakaninsu.

Kiran na zuwa ne a daidai lokacin da yajin aiki direbobin babur din suka fara a Jihar ranar Litinin ya shiga yini na uku.

Sakataren Zauren, Dokta Sa’id Ahmad Dukawa ne ya bayyana hakan a zantawarsa da Aminiya.

Dokta Dukawa ya bayyana cewa Zauren ya damu matuka da halin haula’in da yajin aikin na matuka baburan ya jefa al’ummar Jihar.

A cewarsa, “Kasancewar wannan yajin aikin ya shafi zirga-zirgar ’yan makaranta da ma’aikata da ’yan kasuwa da marasa lafiya masu zuwa asibiti da sauran al’ummar gari masu bukatu daban-daban, Zauren ya damu matuka da irin hali da al’umma suka shiga a sanadiyyar yajin aikin, musamman duba da yanayin da dama ake ciki na kunci da matsin halin rayuwa.

“A dalilin hakan, Zaure yana kira ga gwamnati da matuka baburan da su yi la’akari da yanayin da dubban mutane suka fada, su gaggauta zama tare don bibiyar matsalolinsu tare da warware su cikin ruwan sanyi.”

Har ila yau Zauren ya jaddada rokonsa ga bangarorin biyu da su dubi Allah da masalahar BayinSa domin kawo karshen wannan danbarwar.

Zauren kuma ya yi kira ga al’ummar Jihar Kano da su ci gaba da hakuri
tare da addu’ar neman Allah Ya kawo karshen wannan matsala tare da sauran matsalolin da suka addabi al’umma.