Yajin aikin da direbobin babur mai kafa uku da aka fi sani da Adaidaita Sahu a Jihar Kano suka tsunduma ranar Litinin ya yi sanadiyyar tafka asara ga direbobin da gwamnati da ma ’yan kasuwar Jihar ta miliyoyin Nairori.
Aminiya ta rawaito cewa wannan shi ne karo na biyu da ’yan Adaidaita Sahun ke tsunduma yajin aiki a cikin kasa da wata 12, lamarin da yake shafar tattalin arzikin da walwalar jama’a.
- Tsohon Shugaban Kasa, Ernest Shonekan, ya rasu
- Shugaban Majalisar Tarayyar Turai, David Sassoli, ya rasu
An kiyasta cewa yajin aikin na ranar Litinin ya sa gwamnati ta yi asarar kusan Naira miliyan shida na kudaden harajin da take karba daga wajensu na N100 a kullum, in an yi la’akari da babura 60,000 din da aka ce suna aiki a Jihar a hukumance.
A nasu bangaren kuwa, direbobin sun kiyasta yin asarar kusan Naira miliyan 300, kamar yadda wasu daga cikinsu suka ce sukan yi cinikin tsakanin N5,000 zuwa N7,000 a kullum.
Suna yajin aikin ne dai a kan wata doka ta Hukumar Kula da Ababen Hawa ta Jihar Kano (KAROTA) da ta bukaci sabunta izinin tuki ga dukkan direbobin a kan N18,000 ga sababbi, sai N8,000 ga tsofaffi a kowacce shekara.
Shugaban Hadaddiyar Kungiyar Direbobin Adaidaita Sahun, Sa’idu Dankoli ya ce tun da farko gwamnatin ta yi yunkurin sanya izinin tukin a kan N20,000 ne, kafin daga bisani ta rage shi zuwa N8,000 bayan sun shiga tsakani.
“Bayan mun shiga tsakani, gwamnati ta rage shi zuwa N8,000. Amma duk da haka, mun bukaci a sake ragewa, lamarin da ya sa aka shiga takun saka tsakaninmu da shugaban KAROTA saboda mun ce ya yi yawa.
“Ita kanta gwamnatin ta jinjina wa kokarinmu na biyan haraji na yau da kullum. Ina jin ko saboda haka, ya kamata ta saurare mu,” inji Shugaban.
Ya ce a Jihar ta Kano, suna kiyasin akwai baburan kimanin 70,000 da ke harkoki da su a fadin Jihar.
Amma Kakakin hukumar ta KAROTA, Nabilusi Abubakar Kofar Na’isa, ya ce alkaluman baburan da suke da su a hukumance su ne guda 60,000, la’akari da kudaden harajin da suke karba a kullum.
Ya ce mutanen da suka sabunta izinin nasu yanzu sun kai 10,000, inda ya ce har yanzu suna tsammanin tara Naira miliyan 400 daga ragowar babura 50,000.
Shugaban KAROTA, Baffa Babba Dan-Agundi, ya shaida wa Aminiya cewa direbobin baburan sam ba sa girmama dokokin hanya, kuma ba sa son biyan harajin nasu na yau da kullum.
Ya ce wannan ne makasudin da ya haifar da rashin fahimta tsakaninsu da gwamnatin.
“Gwamnati na yunkurin samar da mafita, saboda muna jin kamar an kyale harkar sufuri a hannun ’yan Adaidaita Sahu su kadai a Kano,” inji Baffa.