✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yajin aiki: Sai mun ga abin da ya ture wa Buzu nadi — ASUU

ASUU dai na zargin Ministan Kwadago da yin baki-biyu

Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU) na zargin Ministan Kwadago, Chris Ngige, da yin baki biyu a zaman tattaunawarsu na baya, inda suka ce suna na kan bakarsu ta ci gaba da yajin aiki.

Shugaban kungiyar na kasa, Farfesa Emmanuel Osodeke, ne ya bayyana hakan ranar Talata, inda ya ce ba za su amince da yaudarar Gwamnati ba.

Kalaman shugaban na zuwa ne bayan Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari ya ba Ministan Ilimi da na Kwadago, da Sakataren Gwamnati, umarnin zama da kungiyoyin domin samar da matsaya kan tataburzarsu da Gwamnati.

To sai dai shugaban ASUUn ya ce ya zamo dole su wayar wa da al’ummar Najeriya kai kan halin da ake ciki, wanda ya ce tun farko gwamnatin ce ta jawo shi.

Ya ce: “Mu kungiyoyin masu ilimi ne, da tabbatattun hujjoji muke amfani, don haka dole mu sanar da mutane halin da muka rabu da su a duk zamanmu na baya.

“Kada a manta da maganganun da Shugaban Kasa da sauran bangarorin Gwamnati suka yi a baya-bayan nan, musamman ma wadanda Ministan Kwadago ya yi na cewa babu wata yarjejeniya tsakaninmu da su, da kuma wai mun zauna mun tsara albashinmu ba da su ba, ban da cewa mun bukaci wakilan ma’aikatun gwamnati da hukumomi da su ceci kansu daga tattaunawar.

“Mun zauna sau da dama da Ministan Kwadago, amma babu wani tartibin abu da muka cimbma, sai kwan-gaba kwan-baya.

“Misali sai ya fito kiri-kiri ya nuna yana goyon bayan a biya mana bukatunmu na shekarar 2009 cikin watanni shida, sai kuma ya zo da wata maganar daban bayan nan.

“Da muka bayyana masa damuwarmu kan yadda tattaunawar ke tafiyar hawainiya, sai ya budi baki ya ce shi fa ba shi ya dauke mu aiki ba, mu tafi ga Ministan Ilimi shi ne ya fi dacewa da sabgarmu.”

Wannan dai na daga cikin hujjojin da shugaban ya bayyana a matsayin dalilansu na kin janye yajin aikin.