✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yajin aiki: Likitoci sun cimma yarjejeniya da gwamnati

Ministan Kwadago ya yi alkawarin gwamati za ta yi duk abin da yarjejeniyar ta kunsa

Gwamnati Tarayya da Kungiyar Likitocin ta Kasa (NARD) sun sanya hannu a kan yarjejeniya domin kauce wa shigar likitocin yajin aiki.

Bangarorin sun cimma yarjejeniyar ce bayan wani dogon zama da suka yi da Ministan Kwadago, Chris Ngige, sa’o’i kadan kafin cikar wa’adin yajin aikin da likitocin suka sanya, ranar 1 ga Afrilu, 2021.

“Yarjejeniyar ta ce za ku yi magana da mambobinku, muna fata idan kuka zo karbar kwafinku za ku sanar cewa ba za ku shiga yajin aikin ba,” inji Ngige ga Shugabannin likitocin, bayan zaman nasu.

Zaman ya tattauna kan alawus-alawus din likitoci, albashin da suke bin ba shi, hakkokin wadanda suka rasu a yaki da cutar COVID-19 da kuma neman karin alawus din masu yin aikin da dai sauransu.

Ngige ya ba da tabbacin cewa za a aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma da likitocin.

“Awa 12 ba karamin lokaci ba ne. Kowane bangare zai rika aiki. Kungiyar Likitoci ta MDCN za ta ci gaba da gudanar da aiki.

“Muna sa ran gobe, kamar yadda aka yi alkawari a nan, za a biya rukuni na biyu na likitoci. Kuma idan aka fara a goben muna sa ran za a gaba.

“Muna so idan Shugaban Likitocin Asibitoci ya kawo jerin sunayensa na karshe aka hada da na MDCN, ya zama babu wasu likitocin da ba a biya ba.”

Ya ce an taron ya kuma sanya wa’adin biyan sauran bukatun likitocin da aka tattauna a lokacin zaman; don haka bangarorin za su sake zama domin ganin yadda aka aiwatar da yarjejeniyoyin da aka kulla.

“Muna fata da wannan yarjejeniyar, za su fahimtar da mambobinku cewa tun kafin ku zo gwamnati ta yi hobbasan magance matsalolin.”

A cewarsa, hakan da gwamnatin ta yi, shi ne zai magance matsalar da lokitocin suke yin korafi a kai.

“Mun ji dadi da ganin kun fahimta. Ina tabbatar muku cewa za a aiwatar da duk abubuwan da ce cikin yarjejeniyar.

“Za kuma mu taimaka wa Ma’aikatun Lafiya, Kudi da Ofishin Akanta-Janar na Tarayya su yi nasu bangaren domin kawo karshen wannan tankiyar.”